Kamar yadda muka sani, AI (artificial intelligence)  ya shiga cikin ko wane ɓangare na al'amuran Yau da kullum, kamar harkokin lafiya, kasuwanci, kirkira, da dai sauransu.

A bangaren sarrafa hotuna ma AI yana taka muhimmiyar rawa wajen gyara hotunan da muka ɗauka da wayoyin mu, su Zama Masu kyau da ɗaukar hankali!, Kai tsaye abun da zan koyar da Kai kenan a cikin wannan rubutu.




Mataki na 1:

Ka garzaya a duk wata kafa da zaka iya amfani da ita domin kirkiran kayataccen hoto Da ai ta hanyar rubutu,  se kayi amfani da wannan rubutu, ko ka Kirkire naka!.


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


 A photo realistic of a 25-year-old Nigerian Hausa man with a brown skin tone.

He has a beard . He is wearing a white Hausa traditional attire and Hausa Cap and black shoes. He is standing in front of a luxury car Lamborghini blue color.   

☝️☝️☝️☝️

Wannan zai baka damar kirkirar hoto Mai kyau Kamar wannan



Mataki na 2

Ka shiga kamera na wayar ka se ka dauki hoton fuskar ka


Mataki na 3

Kaje a akwatin nema na Google ka rubuta wannan Kafa REMAKER.AI, se ka danna alamar nema.

Ka tabbatar ka zabi FACE SWAP, se ka danna wurin photo na farko, ka aza hoton da ka kirkira da AI.

Ka danna alama ta ta kasa, ka saka hoton ka da ka dauka da wayar ka, se ka danna madanni na SWAP.

Ka jira zuwa sakanni 20 secs zaka ga fuskar ka ta koma ga hoton da Ai ya kirkira 🥰


RUFEWA:-

Wannan itace hanya mafi sauki da zaka gyara hotunan ka, kuma zaka iya amfani da wannan hanya ka Kirkire hotuna masu kama ɗaya, wanda zai taimaka kwarai ga Wanda yake so ya kirkiri Wani wasan kwaikwayo da AI.

Ku danna nan domin kallon video