gabatarwa

A cikin wannan rubutu zan nuna muku yadda zaku kirkiri haɗadden bidiyo na TIKTOK, wanda zaku samu mabiya da yawa, ta hanyar amfani da chatgpt Domin kirkirar labarai, da kuma amfani da COPILOT AI Domin kirkirar hotuna da zamu hada cikakken bidiyo na labarai domin samun mabiya a TikTok .




Yadda zaku kirkiri VIRAL TIKTOK VIDEO 
Daga farko zamu bi matakai uku ne domin Samar da TikTok video da zai samu mabiya.

Step #1: yadda zaka kirkire labari mai jan hankali a TikTok!.

Kirkirar labarai masu jan hankali a TikTok yana bukatar tsayawa ayi tinani mai zurfi da kuma Samar da labari wanda zai ja hankali, se dai wannan abu ne mai wahala ga Wanda shi ba marubucin labari bane. A cikin wannan sabon rubutu zan nuna muku yadda zaku Yi amfani da chatgpt wurin kirkirar  TikTok viral video.

Yadda zaku kirkiri labarai da chatgpt 

Daga farko kaje a playstore ka sauke manhajar chatgpt, ko ka garzaya a yanar Gizo ka bincike  chatgpt Domin farawa.
Email kawai kake bukata se lambar waya! Domin bude chatgpt account.

Bayan ka buɗe account a chatgpt wannan shine fegi na farko da zaka ci karo dashi.
Kaje a cikin akwatin sako ka rubuta Duk kalar labarin da kake so chatgpt ya kirkira maka!, Abin burgewa shine, chatgpt zai iya fahimtar Yaren Hausa kuma ya rubuta labari da Yaren Hausa , ka kammala siffanta irin labarin da kake so se ka danna kibiyar tura sako . 
Domin saukake muku aiki na samar maku da rubutun da zaku yi amfani da shi domin kirkiran labari da chatgpt kuma ya baku prompt da zaku kirkiri hotuna da kowane ai cikin sauki.

Ga prompt ɗin:
" Ka dauka cewa kai content creator ne kana da TikTok account da zaka na ɗora bidiyoyi na labaran Africa masu jan hankali, wasa ƙwaƙwalwa, ban dariya da kuma ban al'ajabi!.
Aikin ka a yau shine ka "Kirkire gajeren labari mai ban mamaki da kuma ban dariya".

 Kayi amfani da salo irin na littafin " Magana jari "
Ka Kirkire MATASHI MAI JAN HANKALI SOSAI AKAN LABARIN (TITLE).

Ka tabbatar ka samar da ingantaccen prompt! A karshen ko wane sashe na labarin , prompt ɗin ya kasance a cikin harshen turanci domin kirkiran hotuna da Ai, kuma ka tabbatar hotunan zasu zama masu kama iri daya, sabo da guje wa (inconsistent character).

Tunatar wa: prompt ne kaɗai zai kasance a cikin harshen turanci, amma labarin a yaren Hausa zai kasance!".

Ka canza wannan da irin labarin da kake so a cikin rubutun da ka kofa "Kirkire gajeren labari mai ban mamaki da kuma ban dariya".

Yadda zaku kirkiri labarai da chatgpt

Step #2: yadda zaku kirkiri hotuna da COPILOT a WhatsApp

Bayan kun kirkiri labarai da chatgpt mataki na gaba shine kirkirar hotuna.
Yadda zaku yi shine, koyi kofi na prompt da chatgpt ya rubuta, se kuje a WhatsApp ku saka wannan rubutun da kuka kofa, ku danna wannan Link domin domin amfani da COPILOT kai tsaye.
https://wa.me/message/TJ5MI22N6WUVD1

Yadda zaku kirkiri hotuna da COPILOT 
.

Step #3: yadda zaku nadi sauti kuma ku haɗa video.

Bayan kirkirar hotuna a COPILOT, mataki na karshe shine yadda zaku haɗa Muryar labarin da kuka kirkira a chatgpt, kuma ku haɗa hotuna waje daya domin haɗa cikakken bidiyo.

A cikin wannan zaku iya amfani da capcut ko duk Wani video editor da kake amfani da ita.
A cikin wannan zanyi amfani INSHOT , Bayan ka buɗe video editor kaje ka dauko hotunan da ka kirkira da COPILOT, se ka saita su ɗaya bayan ɗaya, ka tabbatar ko wane hoto ya tsaya inda ya kamata domin kayatarwa!.

Se ka danna wajen voice, kaje ka Fara recording na labarin da chatgpt ya kirkira bayan ka kammala, se kayi exporting na video dinka ka fara posting.
Domin ƙarin fahimta ku kalli video Na a YouTube

RUFEWA:

A cikin wannan Post mun koyi yadda zamu kirkiri labarai da chatgpt, kuma mu kirkire hotuna da COPILOT, Sa'an nan mun koyi yadda zamu nadi sauti da manhajar gyaran video .
Wannan ze taimaka ma sosai wajen kirkiran cikakken bidiyo da zai samu mabiya da yawa a TikTok, YouTube, da Instagram.