Kirkirar hotuna da Ai ya zama wani Abu da yake taimakawa mutane a wajen tafiyar da harkokin kasuwanci su ta hanyar kirkiro hutuna masu jan hankali wanda suke taimaka musu wajen bun kasa kasuwanci!.


Kamar haka ma kirkirar video da AI ya zama Wata hanya ta saukake ma mutane hanya wajan video editing, finafinai da sauran su.
Mai makon bata awowi kana ɗaukar video, to yanzu zaka iya amfani da AI ka Kirkire wannan video cikin Yan mintuna.
 
AI movie video

Misali Zaka iya kirkirar video domin ɗorawa a shafin social media kana samun yan kudade, kuma zaka iya amfani da shi domin tallata kasuwancin ka ko burgewa ga abokan ku.

Yadda zaku kirkiri video da AI

Abubuwa biyu kake bukata domin domin kirkiran bidiyo da Ai.

Na daya 1

Ka tanadi script wanda kake so ka Kirkire video Akai, misali labarin da da kake so ka isar a cikin wannan video.
Script kai tsaye yana nufin labarin da kake so ka Kirkire video Akai ko kuma hotunan da kake so ka mayar da su zuwa bidiyo.
 A cikin wannan koyarwar zanyi amfani da wannan rubutu domin kirkiran irin video dake sama, kaima zaka iya kofi domin kayi amfani da shi.

✏️✏️✏️✏️
A scene of a 3d render boy standing in front of a big gorilla 🦍 in a dark forest, and a Big dark monster jumping over to catch the boy but the gorilla protecting him,the boy was scared , wearing War garment trying to shoot the monster with magic arrow ".

Na biyu

Yi amfani da Ai tool text to video AI model domin kirkiran bidiyo ka.
A cikin wannan koyarwar zanyi amfani da wani ai tool mai saukin aiki da kuma bada sakamako Mai kyau.
Akwai ai da dama da zaka iya amfani dasu ka kirkiri bidiyoyi, amma dai wannan yana daga cikin mafi sauki da na taɓa amfani da su!.
Ka danna wannan Link na minimax Ai , zai ɗauke ka zuwa inda zaka kirkire account, se kaje ka buɗe account ta hanyar amfani da email ko kuma ka danna "continue with Google ".

🔗🔗🔗🔗🔗🔗
https://hailuoai.video/

Zasu lamunce maka kwanaki Uku da Zaka iya kirkirar video ba adadi har iya son ranka, amma daga baya Zaka iya kirkirar video Uku ne kacal a rana, amma kyauta ne🤫.

Rufe Wa 

Kada ka manta, kirkirar video mai kyau yana da alaƙa da kwarewar ka bangaren iya amfani da Ai model, ba lalle ka samu sakamako mai kyau irin nawa ba ko idan ba ka iya yin amfani da shi ba.