Nasan zai iya yiwuwa ka taba gani internet, ko ka taba ji a bakin mutane akan cewa ana samun maƙodan kuɗi online ta hanyar kir-kirar website domin yin blogging!!.
Babu shakka wannan hakane ana samun kuɗi online sosai ta hanyar kir-kirar website da kuma sana'ar blogging, domin kuwa zaka iya samun a ƙalla 100k a Duk Wata ta hanyar blogging.
Se dai babban kalubale shine:
- Shin menene website?
- Ta yaya ake kir-kirar website?
- Yaya website take aiki?
- Ya ake samun kuɗi da website?
Wa yannan abubuwa ba ko ina kake samun cikakken bayani ba akansu , kamar yadda zanyi bayani sosai a cikin wannan rubutu, domin kuwa a cikin wannan rubutu zanyi bayani kwatta kwatta akan :
- Minine website
- Yadda website take aiki
- Yaya ake kir-kirar website domin samun kuɗi online
- Kashe kashen website.
Ba tare da bata lokaci ba, Yana da kyau
1. Minene website?
Website na nufin wasu tarin shafukan yanar gizo ne da ke dauke da Bayanai akan Wani abu, kuma wa yannan pages zava iya neman su a internet ta hanyar adreshin wannan website, wato (domain) . Shafukan yanar gizo galibi ana sadaukar da su ga wani batu ko manufa, kamar labarai, ilimi, kasuwanci, nishaɗi ko sadarwar zamantakewa.
2. Yadda website take aiki.
Kamar yadda muka faɗa a baya, website tarin shafuka ne da suke dauke da Bayanai Kuma za'a iya nemo wa yannan bayanan ta internet wato browsing.
Yadda website take aiki shine aduk lokacin da wani yayi Searching na wani bayanai a wani search engine, (Misali google) internet ta hanyar browser (misali, chrome, opera, safari da sauran su), to kai tsaye search engine zai tura wannan request zuwa ga server.
Me nene server?
Server gidan yanar gizo software ce da kayan aikin da ke amfani da HTTP (Hypertext Transfer Protocol) da sauran ka'idoji don amsa buƙatun abokin ciniki da aka yi akan Yanar gizo ta Duniya (www). Babban aikin server gidan yanar gizo shine nuna abubuwan gidan yanar gizon ta hanyar adanawa, sarrafawa da isar da shafukan yanar gizo ga masu amfani.
A Duk lokacin da kayi searching na wani abu a internet, daga Farko google zai tura wannan rubutun da aka yi zuwa ga server, ita kuma server se ta duba bayanan da kake nema se ta mayarwa search engine da ansa, daga nan ne zakaga Abin da kake nema ya bayyana akan peji🤔.
3 . yadda ake kir-kirar website domin samun kuɗi online.
Asali Kirkirar website abu ne da yake bukatar ilimin computer programming, Misali HTML, CSS, JAVASCRIPT, PHP da de sauransu.
Amma da yake zamani yana ci gaba da zuwa da hanyoyin saukaka al'amurran rayuwa, akwai hanyoyi Masu matukar sauki da zaka kir-kiri website cikin yan sa'o'i kaɗan akwai wa ƴanda suke kyauta ne akwai kuma wa ƴanda se ka biya .
A cikin wannan website inshallah zan kawo hanyoyi da zaku mallaki website a kyauta, 🥳, daga Farko zan kawo hanyoyi da zaku mallaki professional website a kyauta, sa'annan zan nuna hanyoyi da zaku biya a yi muku professional website dai dai yadda kuke bukatar ta, fatana shine ku kasance a tare damu.
A kwai hanyoyi Uku da zaka mallaki website a kyauta ✅.
- Blogger
Blogger.com wuri ne mafi sauki da zaka mallaki professional blogging website a kyauta, zaka iya customizing dinta Duk yadda kake so , kuma zaka iya monetize na wannan website da adscence da adstera ko affiliate marketing domin samun kuɗi da ita.
Zaka iya amfani da Duk wani ads provider domin samun kuɗi da website dinka ba tare da ka wahala da yawa ba.
Babban Misali shine, wannan website da kake karanta wannan bayanan an kirkireta ta ne da blogger, wacce ita kuma blogger ɗin mallakar kamfanin google ce
2. Wordpress
Wordpress kusan itace lamba ta ɗaya a cikin wuraren da ake kir-kirar website a kyauta.
Domin kirkirar taka website a yau, kai tsaye zaka iya danna wannan Link domin farawa.
A cikin post na gaba zan yi bayani step by step kan yadda ake kir-kirar website a blogger da kuma wordpress.
Hanyoyi biyu da ake biyan kudi domin mallakar website.
1. Daukar hayar wani professional web developer Domin ya kir-kirar maka website, kalar wacce kake so kuma yadda kake so.
Zaku iya samun irin wadannan mutane da zasu yi maku aiki ku biya a wurare kamar haka.
Fiverr, legiit da dai sauransu.
2. Marketplace.
Marketplace wurine da kowa ke zuwa ya kasa hajar sa.
A Irin wannan website zaka ga website, application kala kala daga mutane da daban daban ko wanne da irin farashin sa, so nan ma hanya ce ske mallaka website..
3. Ai website builder
A kwai platforms da dama da suke ba mutum damar kirkirar website a cikin ya seconds, kamai 10web, da iri irin su.
Kashe kashen website.
Akwai website kaloli daban-daban, Daga ciki akwai:
- Blogging website
- Online tools website
- School website
- Company website
- Da dai saura
Daga ƙarshe:
Wannan shine takaitaccen bayani akan website da yadda take amfani.
Ku kasan ce tare damu a post na gaba domin kuwa zanyi bayani akan website zamu



0 Comments