Assalamu alaikum wa rahmatullah dan uwa mai karatu!, nasan ka sha ganin wasu bidiyoyi da suke yawo akan social media, wanda zaka ga hoto yana magana, ko karatu ko makamancin haka.




A cikin wannan rubutu ba Zan nuna maka yadda zaka saka hoto magana bane kawai, a, a zan nuna maka yadda zaka kirkire hoton mutum katun ko duk abun da kake so ta hanyar amfani da text-to-image AI modal, sa'annan zan nuna maka yadda zaka saka hoton yayi magana, ba wannan kaɗai ba Zan nuna maka yadda zaka iya kirkirar cartoon film ta wannan hanyar zaka iya kirkirar channel, Kuma YouTube suyi monetization dinka. 

Kenan zaka koyi yadda ake kirkirar hoto, yadda ake saka hoto yayi magana, yadda ake nadar sauti (voice recording) da sound editing da sauran su lyadda ake editing a mayar da shi Film.


Kalli Wannan wannan misali 👇


Yadda ake mayar da rubutu zuwa hoto -text to image


A cikin wannan tutorial zamuyi amfani da adobe firefly Domin mayar da rubutu zuwa hoto.

Ku danna wannan Link domin buɗe account a adobe firefly a kyauta.

 za su baku kyautar 25 credit a kowane Wata, zaku iya amfani da wannan credit Domin kirkirar hotona.

Yadda ake kirkirar hoto a kowa ne Irin text to image AI model kake amfani dashi hanya ce mai sauki, ko wane ai model yana kirkirar maka hoto ne gwargwadon fahimtar da yayiwa rubutun da ka rubuta masa, ma'ana yadda ka siffanta hoton.

Bayan kun bude account, ku danna akan text to image, se ku rubuta wannan prompt a cikin akwatin rubutu:

Prompt:

" 3D render baby standing, adorable big eyes, in a garden with butterflies, lush greenery

Se ku danna wannan button mai alamar tauraro .

Zai baka result na hoton yara, se ka bi matakan da na nuna acikin wannan video.




Daga karshe zaka samu wannan hoton.



Yadda ake saka hoto yayi magana 

Domin saka wannan hoton yayi magana, zamu yi amfani da wannan APP Mai suna dreamface . 





Daga fako zaka yi downloading na dreamface APP, sa'annan  ka danna akan talking > , se ka zaɓi hoton da zaka saka shi yayi magana, se ka danna continue  > ,  daga Nan Zaka ga an baka damar yin rubutu ko sautin Muryar da kake so wannan hoton yayi magana dashi, Daga nan se ka danna animate, Zaka ga hoton yana magana kamar haka:-


Ku danna wannan Link domin downloading na dreamface APP
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.dreamapp.dubhe.

Kirkirar Short film ta wannan hanyar abune da yake bukatar dogon lokaci, saboda haka, zamu ɗora daga nan a rubutu na gaba ko kulli wannan video https://youtu.be/Tnkojwm2LBM domin cikakken bayani.

Ku biyoni domin ci gaba a rubutu na gaba.

Abubuwan da muka koya:-


  1. Yadda ake mayar da rubutu zuwa hoto.
  2. Yadda ake saka hoto yayi magana.

Rufewa:
A cikin wannan tutorial min karu da ilimin yadda ake kirkirar hoto ada ai wato artificial intelligence , da kuma yadda ake saka hoto yayi magana.