Gabatarwa:

Idan har ka bibiyi posting da nayi a baya, nasan ka fahimci mice ce website kuma, da kuma yadda website take aiki.



A cikin wannan sabon Post zanyi bayani dalla dalla yadda ake buɗe blogger website domin samun kuɗi ta hanyar blogging.

A dai dai wannan lokaci na digital marketing, website tana matukar muhimmanci ga daidaikun mutane da kuma kasuwanci. Website wuri ne na watsa idea da ra'ayoyin ku, ko kayan tallace tallacen ku a duniya domin kowa ya sani.

Wata kila Kai sabone game da al'amarin kirkirar website, Kuma kana neman wuri mai sauki da zaka iya mallaka website!, Blogger itace zaɓi mafi fici. A cikin wannan post zan yi bayani cikakken a kan yadda ake bode website a blogger.

Step 1: yadda zaka bude blogger account.



Domin farawa ka danna wannan rubutu (Blogger) se kayi signing da google account dinka.

Idan ba kada google account zaka iya kirkirar sa cikin sauqi ta wannan Link.

Bayan kayi signing da google account dinka a blogger.com kai tsaye se ka danna akan "create new blog" se ka fara process na ƙirƙirar website.

Step 2: mataki na gaba shine ka zabe suna mai kyau da zaka sakawa website ɗin ka.



 Yanada muhimmanci ka zaɓi suna mai ma'ana kuma mai sauki, wanda zai yi dai da Abin da kake so ka yi sharing a website ɗinka. Misali, Ni sakawa wannan website suna "pintricks", saboda ina so in rica sharing na wasu online tricks masu muhimmanci da zaku amfana dasu.

Bayan ka zaɓi suna da ya dace website ɗinka , abu na gaba shine ka zabar wa website dinka URL address, Wato adreshin website dinka kenan.  Asali de yadda URL address yake zuwa a blooger shine (yourblogName.blogspot.com) misali (duniya.blogspot.com) amma zaka iya canja wannan kamar yadda nayi a wannan website.

Image from fasaha blogs


Ka tabbatar ka zabi suna mai ma'ana kuma wanda zaka iya tunawa.


Step 3: zabar template.



Blogger tana bada damar zabar template da dama, wa ƴanda zasu yi dai dai da abin da kake so Kayi da website dinka. Template shine zai ba website dinka damar yin kyau sosai,  kuma tayi dai dai da abin da kake so Kayi da website ɗin.

Zaka iya bincika a cikin jerin template din domin kaga wanda style dinsa zai yi kyau da website dinka! Zaka iya canja shi a duk sanda kaso daga baya.

Step 4: design da kuma tsara website dinka.




Bayan ka zabi template, abu na gaba shine tsara website dinka, wato customizing kenan.
Ka danna "layout" ka je zuwa blogger dashboard zaka options da dama da zaka iya canja tsarin website dinka yadda kake so.
Ta Nan ne zaka iya saka wa ko cire Wani element, kamar : header, footer, sidebar, Babbar, da dai sauransu. ta hanyar amfani da tsarin s drop-down.
Zaka iya canja, background, tsarin rubutu, kaloli daban-daban ta yadda website dinka zatayi kyau sosai.

Step 5:  yadda ake kir-kirar page da kuma post a blogger.



A yanzu tunda ka riga ka tsara website dinka, Abu na gaba da ya kamata ka sani shine yadda ake kir-kirar sabbin pages da kuma yadda zakayi posting a cikin website dinka.

Page dai  kai tsaye wuri ne da ake posting na wasu bayanai ko wani tsari, kamar "contact us " page "about" page, ko kuma wasu bayanai da ba kai tsaye zaka canja su ba.
A sashe daya kuma , posts suna amfani ne wajen rubuta articles ko labarai, ko wasu update 🔥 masu amfani.
Ki a tsaye zaka iya kirkirar sabon page ko Sabon Post ta hanyar danna wa akan "page" ko "Post"a cikin blogger dashboard, se ka zabi "New page" ko new Post".

Step 6: yadda zakayi publishing da kuma sharing na website dinka.



Kafin ka gabatar da website dinka ga jama'a, ya kamata ace ka duba ta Wato "review" ta hanyar amfani da review option a cikin blogger dashboard kamar yadda kake gani a cikin wannan hoton. Bayan ka tabbatar website dinka tayi yadda kake so, se  danna "publish" domin website din taje live akan internet.
Kayi sharing na website dinka da family ka da abokan ka da sauran social media domin tara mabiya, wa ƴanda sune zasu taimaka maka wajen cimma burin ka na samun kuɗi online da wannan website ɗin.




Step 7: managing da kuma haɓakar website dinka.

Bayan kayi launching na website dinka akan internet, abun da zaka yi shine ka tabbatar kana managing na website ɗin da kuma updating ɗin ta akai akai.
Blogger ta samar da kayan aiki Masu saukin amfani da zasu taimaka maka wajen kula da website dinka, kamar updating na pages, posting, da dai sauransu ka tabbatar kayi sharing na website dinka domin ƙarin 
masu ziyarar tar ta.

DAGA KARSHE:

Kirkirar website a blogger abune mai sauqi sosai kamar yadda ka gani, musamman ga wa ƴanda yanzu suke son farawa. Bugu da kari ga kayan aiki da zasu taimaka maka wajen tsara website dinka. Zaka iya tsara website ta musamman kuma ta ji da gani a cikin lokaci daya.
Kada ku manta da zabar suna mai kyau mai sauki wanda zai yi dai dai da website ɗinku. Ku zaɓi template mai kyau wanda zai karawa website ɗinku armashi.

Ta hanyar bin wa yannan tsarukan da na lissafa da kuma updating na website dinka zaka yi farin cikin gina website mai kyau da kuma armashi.

Congratulations for building your first website!